Isa ga babban shafi
Singapore

Trump ya bayyana samun nasara a taronsu da Kim

Shugaban Amurka Donald Trump a karon farko ya gana da shugaban kasar Koriya ta Arewa Kim Jong Un a kasar Singapore, inda shugabannin suka fara tattaunawa kan kulla dangantaka da kuma yadda za’a shawo kan kasar ta kwance damararta ta Nukiliya.

Musabahar shugaban kasar Amurka da shugaban kasar Korea ta Arewa Kim Jung Un
Musabahar shugaban kasar Amurka da shugaban kasar Korea ta Arewa Kim Jung Un SAUL LOEB / AFP
Talla

Shugabannin biyu sun fara musabaha a gaban manema labarai, kafin daga bisani suka shiga wani daki su biyu tare da masu yi musu fassara inda suka gana.

Yan jaridu da aka gayyata sun yi ta daukar hotuna, a haduwar farko ta shugaba Donald Trump da Kim Jong Un kamin su gana a yau.

Ita dai wannan ganawa da duniya ta zuba ido ta ga yadda za ta gudana, an fara ta ne a asirce, bayan shugabannin sun yi musabaha a gaban kadan daga cikin manema labaran da aka gayyata.

Daga bisani shugaba Trump da Kim sun shige wani daki, inda suka tattauna su biyu tare da masu masu fassara, kafin daga bisani su koma wani daki tare da jami’an su.

Bayan wannan ne suka gana da manema labarai, inda shugaba Trump ke bayyana cewar.

“Ina mai matukar farin ciki, kuma zamu samu tattaunawa mai muhimmanci, kuma ina ganin za’a samu gagarumar nasara, kuma fata na itace samun dangantaka mai matukar tasiri”

A nashi martanin, shugaba Kim Jong Un yace hanyar da aka bi kamin kai ga ganawar tasu ba mai sauki ba ce, ya kara da cewa.

“Hanyar zuwa tattaunawar nan ba mai sauki bace, irin matakan da aka dauka baya, sun zama shinge kan hanyar mu ta samun cigaba, amma yanzu mun kauda su, kuma gamu a nan yau”

Yanzu dai duniya ta zuba ido ta ga abinda zai biyo bayan wannan ganawar ta farko, da masana harkokin Diflomasiyya ke gani a matsayin dodorido, musamman lura da bukatun Amurka da kuma matsayin da kasar Korea ta Arewa ta kai na kera makaman kare-dangi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.