rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Faransa Emmanuel Macron

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Macron na gaf da yin nasara kan shirinsa na sauye sauye a Faransa

media
Kungiyar kwadagon Faransa na SNCF. REUTERS/Christian Hartmann

Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron na gaf da samun nasarar shirin sa na sauye sauye ga harkokin sufurin jiragen kasa wanda ya gamu da mummunar suka daga kungiyoyin ma’aikata.


Kwamitin Majalisar kasar ta amince da matakin karshe na dokar sauya fasalin harkokin jiragen wanda zai bude kofar rage kudaden da ake kashewa da kuma baiwa masu zuba jari damar shiga a dama da su.

Yau ake saran Majalisar wakilai ta kada kuri’a a kan sauyin, yayin da gobe Alhamis kuma Majalisar Dattawa ta kada nata kuri’ar.

Minister sufuri Elizabeth Borne ta bukaci goyan bayan yan Majalisun kan shirin.