Spain Bakin-haure Italiya Hakkin Dan Adam
wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa
Bakin-hauren da Italiya ta kora sun isa Spain

Jiragin ruwan Aquarius mai dauke da bakin-haure 630, da Italiya da haramtawa shiga cikinta, ya isa tashar ruwan birnin Valancia da ke Spain da safiyar yau Lahadi.
A makon da ya gabata ne Spain ta bayyana aniyar taimakawa bakin-hauren mafi akasari da suka fito daga nahiyar Afrika, bayanda Italiya ta hana su isa gabar ruwanta.
Daga cikin bakin hauren akwai mata masu juna biyu 7 da kuma kananan yara 123.
Yawan bakin-hauren da Spain ke karba na ci gaba da karuwa, bayan da a wani aikin ceto da jami’an gabar ruwan kasar suka gudanar, tsakanin ranar Juma’a da Asabar, suka ceto wasu bakin-hauren 933 daga hallaka a tekun Mediterranean.