rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Jamus ‘Yan gudun Hijira Tarayyar Turai

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

An samu sabanin ra'ayi tsakanin Merkel da Ministanta kan 'Yancirani

media
Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel tare da ministan harkokin wajen kasar Horst Seehofer yayin tattaunawarsu a birnin Berlin bayan kalaman da ya fitar kan 'yan cirani wanda ya sabawa kudirin da gwamnatinta ke kai. REUTERS/Fabrizio Bensch

Ministan harkokin cikin gida a Jamus Horst Seehofer ya sha alwashin kulle kan iyakokin kasar ga ‘yan ci rani, nan da watan Yuli mai zuwa matukar shugabar gwamnatin kasar Angela Merkel ta gaza samar da daidaito tsakaninta da takwarorinta shugabannin kasashen Turai kan batun.Sai dai duk da matsin lambar da ta ke fuskanta kan ‘yan ci rani Angela Merkel ta ki amincewa da kudirin.


Merkel wadda ta aike da gargadi ga minista Horst Seehofer ta ce kalman ministan tamkar suna bijirewa kudure-kudiren da gwamnatinta ta sanya a gaba ne.

A cewarta ta na fatan kulla wata sabuwar yarjejeniya da kasashen Turai yayin taron kungiyar EU da za su gudanar daga ranar 28 ga watan nan zuwa 29 ga wata kan ‘yan ciranin, amma fa babu yadda za a yi Jamus ta yi watsi da bayar da mafaka ga ‘yanciranin da suka bukace ta.

Sai dai minista Seehofer wadda ya jima yana caccakar kudirin gwamnatin ta Merkel kan ‘yan ci rani, ya ce ya zama wajibi Jamus ta sauya alkibla kan bakin da ke kwararowa kasar a kowacce rana.

Yayin wani taron manema labarai da ya kira, Minista Seehofer ya ce ko da ‘yan ciranin da Jamus ta hana musu mafaka a baya, yanzu haka suna nan a cikin kasar ba kuma tare da daukar wani mataki ba.

Daga shekarar 2015 zuwa yanzu akwai ‘yan cirani masu neman mafaka fiye da miliyan guda da suka shiga kasar ta Jamus wanda kuma ya yi matukar tasiri wajen raba kan al’ummar kasar haka zalika yayi kwakkwaran nakasu ga jam’iyyar AfD inda ta yi gagarumin shan kaye a babban zaben watan satumba.