Isa ga babban shafi
Turai- 'Yan cirani

Macron da Merkel sun gana kan matsalar 'yan cirani

Shugaban Faransa Emmanuel Macron da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel sun gana a jiya talata, inda suka tattauna batutuwa da dama suka shafi yakin Turai musamman tattalin arziki da kuma matsalar kwararar ‘yan ci-rani zuwa yankin na Turai.

Shugaban Faransa  Emmanuel Macron tare da Shugabar gwamnatin Jamus  Angela Merkel,yayin ganawarsu da ta gudana yau a birnin Berlin 19 ga watan Yuni 2018.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron tare da Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel,yayin ganawarsu da ta gudana yau a birnin Berlin 19 ga watan Yuni 2018. REUTERS/Hannibal Hanschke
Talla

Daga cikin batutuwan da zaman taron na su ya tattauna a kai sun hada ne da sabon rikicin bakin haure da ya haifar da kara farfadowar jamíyu masu raáyin rikau a kasashe da dama na Kungiyar tarayyar turai.

Haka zalika sun tattauna kan batun jirgin ruwan agaji na Aquarius mai dauke da 'yan cirani 630, da aka ceto daga hallaka wanda Italiya ta ki karbarsu.

Yanzu haka dai sabon ministan cikin gidan kasar Italiya Matteo Salvini, shi ne shugaban jamíya mai raáyin rikau ta La Ligue, baya bukatar kasar ta karbi yan ciranin da aka ceto daga teku, al'amarin da ya haifar da ta da jijiyoyin wuya tsakanin Rome da Paris.

A bangare guda itama Angela Merkel na ci gaba da fuskantar tirjiya daga mukarraban gwamnatinta kan kwararowar 'yan cirani kasar wanda su ke alakantawa da abin da ke haddasa yawan tashe-tashen hankula da kasar ke fuskanta.

Ko a dazu da safe sai da shugaban Amurka Donald Trump ya soki gwamnatin ta Jamus inda ya ce sakacin da ta ke na barin bakin haure kwararowa kasar shi ke haddasa rikici a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.