rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Tarayyar Turai Bakin-haure Italiya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Shugabanin Turai na taro don cimma matsaya kan batun bakin-haure

media
Jirgin ruwa dauke da bakin haure a saman teku Hermine Poschmann/Misson-Lifeline/Handout via REUTERS

A yau Lahadi Shugabanin kasashen Turai 16 za su gudanar da taron su a Bruxos domin fayyace daya bayan daya hanyoyin warware batun yan ci’rani dake kokarin haifar da rarrabuwar kawuna tsakanin kasashen.


Faransa ta bukaci a samar da wasu cibiyoyi a Italiya da Spain da za su mayar da hankali domin tanttance ta yada za a iya samarwa yan ci’rani wurare zuwa kasashen da ya dace .

Sai dai Italiya ta bakin ministan cikin gidan ta, ta bayyana adawa, Ministan kasar ya bukaci Shugaban Faransa Emmanuel Macron da ya daina babakere dangane da batun yan ci’rani, Ministan ya bayyana cewa Faransa tana ina a lokacin da jirgin ruwan nan Aquarius ya ja dogon lokaci saman teku kafin Spain ta amince karbar yan ci’ranin a kasar ta.