rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Tarayyar Turai Bakin-haure

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Kasashen Turai na taro kan matsalar baki

media
Shugabannin Kasashen Turai a Brussels Geert Vanden Wijngaert/Pool via Reuters

Shugabannin Kungiyar Kasashen Turai na fuskantar gagarumar rarrabuwar kawuna a taron da suke gudanarwa a birnin Brussels wanda zai mayar da hankali kan baki da makomar kasashen da ke amfani da takardar kudin Euro.


Taron na zuwa ne tare da gargadin cewar, ‘yan ra’ayin rikau da masu adawa da hadin-kan Turai na iya amfani da rarrabuwar kawunan wajen cimma burinsu muddin shugabannin kasashen 28 suka gaza cimma matsaya a tsakaninsu musamman kan matsalar kwararar baki.

Samun gwamnatin da ke adawa da hadin-kan Turai a Italiya da rarrabuwar kawuna kan kasashen da ya dace su karbi bakin, na daga cikin matsalolin da shugabannin za su yi kokarin shawo kansu, yayin da shugaban kungiyar Donald Tusk ke gargadin cewar lokaci na kara kure wa shugabannin.

Shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel ta bukaci kasashen da su yi aiki tare don samar da mafita game da matsalar shige da fice a nahiyar.

Merkel na fuskantar matsin lamba , lura da kalubalen da ke gabanta na gabatar da yarjejeniyar da za dakatar da kwararar baki.