rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Tarayyar Turai Bakin-haure

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Kasashen Turai zasu warware matsalar bakin haure

media
Bakin haure a yankin Turai Kenny Karpov/SOS Mediterranee/Handout via Reuters

Shugabannin Kungiiyar kasashen Turai bayan fuskantar rarrabuwar kawuna mai tsanani, a taron Brussels sun mayar da hankali kan baki da makomar kasashen dake amfani da kudin euro tareda cimma matsaya bai daya.


Taron na jiya Juna’a zuwa ne tare da gargadin cewar yan ra’ayin rikau da masu adawa da hadin kan Turai sunyi kokarin amfani da rarrabuwar kawunan muddin shugabannin kasashen 28 suka kasa cimma matsaya a tsakanin su musamman dagane da abinda ya shafi baki.

Samun gwamnatin dake adawa da hadin kan Turai a Italia da rarrabuwar kawuna kan kasashen da ya dace su karbi bakin da suka isa Turai na daga cikin matsalolin da shugabannin suka shawo kan su, yayin da shugaban kungiyar Donald Tusk ke gargadin cewar lokaci na kara kurewa shugabannin.

Angela Merkel ta bayyana cewa wanan babbar nasara ce zuwa Shugabannin kasahen.

Emmannuel Mcaron Shugaban Faransa ya bayyana fatar sa na ci gaba da samun jituwa a tsakanin su.