rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Faransa

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Wani dan kaso ya gudu cikin jirgi a Faransa

media
Zaman shara'ar Redoine Faid a Faransa bayan kisan wata yar Sanda BENOIT PEYRUCQ / AFP

A Faransa wani dan fashi da ya yi suna a kasar ya tsere da safiyar yau daga wani gidan yari tare da yin amfani da jirgi mai saukar ungulu.


Dan Fashin mai suna Redoine Faid ya na tsare ne a gidan maza da ke yankin Reau daf da birnin Paris.

Faid ya samun taimakon wasu mutane dauke da mugan makamai, wannan dai ne karo na biyu da Redoine Faid ke tserewa daga gidan yari, domin ko a shekara ta 2013, ya gudu daga wani gidan yari da ke Lille –Sequedin a arewacin Paris.

Hukumomi sun sanar da tura ‘yan sanda yankin da aka hango jirgin bayan ficewar Redoine daga wannan gidan kaso.

Kotu ta zartas da hukuncin dauri ga Redoine Faid a shekara ta 2010 na zaman wakafi tsawon shekaru 25 bayan samun sa da laifin kisan wata ‘yar sanda mai suna Aurelie Fouquet.