rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Jamus ‘Yan gudun Hijira Tarayyar Turai Angela Merkel

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Jam'iyyun kawance na barazana ga kujerar Merkel a Jamus

media
Seehofer ya ce bayan tattaunawar da ya yi da jam’iyyar sa, a shirye yake ya aje mukamin sa na minista maimakon amincewa da shirin. REUTERS/Yves Herman/File Photo

Kawancen Jam’iyyun siyasar da ke mulkin kasar Jamus a karkashin Angela Merkel na fuskantar rugujewa sakamakon yarjejeniyar bakin da kasar ta kulla wajen taron shugabannin kasashen Turai a makon jiya.


Rahotanni sun ce baraka tsakanin bangaren shugabar gwamnati Angela Merkel da ministan cikin gida Horst Seehofer ta taso ne bayan kammala taron shugabannin kungiyar kasashen Turai da akayi a Brussels wanda ya amince da shirin kafa sansanonin tantance baki da kuma yadda za’a rarraba su.

Ministan cikin gidan ya kekashe kasa cewar shi bai yadda da shirin karbar bakin da ke iyakar Austria ba da aka yiwa rajista a wasu kasashen Tuari, abinda ke nuna adawar sa da shirin baki daya.

Seehofer ya ce bayan tattaunawar da ya yi da jam’iyyar sa, a shirye yake ya aje mukamin sa na minista maimakon amincewa da shirin.

Bayan tattaunawar da akayi daren jiya, ministan ya ce zai dada ganawa da Jam’iyyar CDU ta Merkel domin ganin ko za su iya cimma wata yarjejeniya yau.

Masu sa ido na kallon ficewar jam’iyyar Seehofer a matsayin wani yunkuri na kada gwamnatin Merkel.