rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Jamus Bakin-haure

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Ministan Jamus zai yi murabus saboda baki

media
Ministan Cikin Gidan Jamus, Horst Seehofer Andreas Gebert / dpa / AFP

Kawancen jam’iyyun da gwamnatin Angela Merkel ke jagoranta na cikin hali na rashin tabbas, bayan da Ministan Cikin Gidan kasar mai tsatsauran ra’ayi, Horst Seehofer ya yi barazanar yin marabus matukar aka gaza cimma matsaya kan yadda za a tunkari matsalar baki a tattaunawar da za su yi a yau Litinin.


Ministan Cikin Gidan wanda ya fito daga wata jam’iyya ta daban, ya bukaci Merkel da ta janye daga tsarin bai wa bakin damar shiga kasar wanda kungiyar Turai ta shimfida wa mambobinta.

A makon jiya ne Mr. Seehofer ya yi barazanar mayar da masu neman mafaka daga kan iyakokin Jamus har sai Uwargida Merkel ta cimma karbarbiyar matsaya da sauran kasashe mambobin Kungiyar Tarayar Turai.

A yammacin ranar Lahadi ne, jam'iyyar CDU ta Merkel ta amince da wani kudiri da ke goyon bayan matsayinta akan tsarin shige da fice a kasar.