rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Faransa

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Kura ta lafa a Nantes bayan zanga-zangar da ta juye zuwa tarzoma

media
Wasu jami'an kashe gobara, a birnin Nantes, yayin kokarin kashe wutar da masu zanga-zanga suka cinna wa wuta. SEBASTIEN SALOM GOMIS / AFP

Hukumomin Faransa sun yi kira da a kwantar da hankula, bayan rikicin da ya barke a birnin Nantes da ke yammacin kasar, sakamakon kisan wani matashi mai shekaru 22 da ‘yan sanda suka yi.


Masu zanga-zangar sun kona motoci 30 da kuma gine-gine bayan da suka samu labarin kisan, yayin arranagama da ‘yan sanda, inda masu zanga-zangar suka rika jifa da kwalaben da aka cinnawa wuta.

Ministan cikin gidan kasar Faransa, Gerard Collomb ya yi tir da tashin hankalin, inda ya ce an dauki dukkatan matakan da suka dace don kawo karshen hatsaniyar.

Wata majiya daga ofishin ‘yan sanda na cewa motar matashin na daya daga cikin motocin da ake sa musu ido kan fataucin miyagun kwayoyi, kuma yayin da ake bincikarsa ne ya nemi tserewa, abinda yakai ga harbe shi wanda kuma ya karasa a gadon asibiti bayan sa’o’i biyu.

Mai gabatar da karar birnin Nantes Pierre Sennes, ya ce, hukumar da ke sa’ido kan laifukan ‘yansanda ta kasa na binciken domin gano gaskiyar al’amari kan yanayin da ya kai ‘yan sandan suka yi amfani da makami.