rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Jamus

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Jam'iyun dake kawance da gwamnatin jamus sun cimma matsaya kan bakin hare

media
Waziriyar Jamus Angela Merkel, à Berlin REUTERS/Hannibal Hanschke

Jam’iyyu uku da ke kawance a kasar Jamus sun amince da sabuwar alkiblar da gwamnatin Angela Merkel za ta dauka domin tsaurara matakai dangane da shigar baki a kasar.

An dai share tsawon watanni bangarorin na na tattaunawa kan wannan batu, kafin cimma jituwa game da wannan shiri, da ke bayar da damar mayar da bakin da suka shiga Jamus a hannun mahukuntan kasashen da suka tsallako domin shiga kasar, yayin da a daya bangare shirin ya amince da kafa wani sansanin tattara baki a kusa da iyakar kasar da Austria.


a ranar alhamis 5 ga watan yuli 2018 a lokacin da take tsakanci kan nauyin da ya rataya a wuyan gwamnatinta  da suka shafi  jinkai  Karar a yau waziriyar jamus angela markel ta bayyana yin hannun riga  ga manufar takwaranta na kasar Hongri Viktor Orban da ya ziyarci kasar ta Jamus , uwargida Markel ta ce za su kare iyakokinsu ta cikin gidan tarayyar turai ne kawai, amma ba akan manufar cewa, su rufe iyakokin gaba daya ba tamkar an  rufe gida ta yadda babu wanda zai shigo