rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Bakin-haure Tarayyar Turai Spain

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Spain ka iya zama cibiyar kwararar 'yan ci rani zuwa turai - EU

media
Wani jirgin ruwa dauke da akalla bakin-haure 233 da kasar Malta ta haramta mishi shiga cikinta. Hermine Poschmann/Misson-Lifeline/REUTERS

Kungiyar kasashen turai ta bayyana fargabar cewa mai yiwuwa Spain ta zama sabuwar cibiyar kwarar bakin-haure daga nahiyar Afrika zuwa nahiyar turai.


Gargadin na wasu jami’an kungiyar ta EU, ya zo ne bayan da kididdiga a bayan bayan nan ta nuna cewa kimanin bakin-haure daga nahiyar Afrika 19,000 suka shiga Spain cikin watanni biyar na farkon shekarar 2018 da muke ciki.

A karon farko kididdigar ta nuna cewa yawan ‘yan ci ranin da suka kwarara zuwa Spain ya zarta wadanda ke isa kasar Italiya a cikin ‘yan watanni, la’akari da cewa ‘yan ci ranin dubu 19 da suka isa Spain a farkon wannan shekara sun kusa kai adadin baki dayan wadanda suka isa kasar cikin shekarar 2017.

Kwarar ‘yan ci rani daga nahiyar Afrika zuwa Spain ya karu ne sakamakon matakin da gwamnatin Italiya ta dauka na rufe dukkanin tashohin jiragen ruwanta daga karbar bakin-hauren da ke ketara tekun Mediterranean don isa cikinta.