rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Birtaniya Diflomasiya Tarayyar Turai Theresa May

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Sakataren harkokin wajen Birtaniya ya yi murabus

media
Tsohon sakataren harkokin wajen Birtaniya Boris Johnson da ya yi murabus a ranar 9 ga watan Yuli na 2018. REUTERS/Simon Dawson

Sakataren harkokin wajen Birtaniya Boris Johnson ya yi murabus daga mukaminsa, matakin da ya zama babbar barazana ga gwamnatin Fira Ministan Birtaniya Theresa May, wadda ke fama da rarrabuwar kai dangane da shirin kasar na ficewa daga karkashin kungiyar kasashen turai EU.


Matakin na Johson a yau Litinin ya zo ne kwana guda bayan da ministan Birtaniyar mai lura da tattaunawar ficewarta daga EU David Davis ya sauka daga mukaminsa.

Murabus din da jiga-jigan gwamnatin Birtaniya, da ke zama babban kalubale ga Fira Ministan Theresa May, ya diga ayar tambaya kan ko shugabar za ta iya kammala aiwatar da manufar ficewar kasar daga cikin kungiyar EU cikin sauki, ko kuma gwamnatinta za ta fuskanci,karin jami’an da za su sauka daga mukamansu anan gaba.

Tuni dai Theresa May ta amince da matakin na Murabus din Boris Johnson, kuma ana sa ran wani lokaci nan gaba kadan za a bayyana wanda zai maye gurbinsa.