Isa ga babban shafi
Amurka-EU

EU ta bukaci Trump ya tuna sadaukarwar da ta yiwa Amurka

Shugaban kungiyar tarayyar Turai Donald Tusk ya bukaci Amurka ta rika girmama abokanan huldarta maimakon mayar da su abokanan gaba.Tusk wanda ke wannan kiran gabanin taron kungiyar tsaro ta NATO da zai fara gudana a Brussels ya ce sadaukarwar da kasashen tarayyar Turai suka yi wa Amurka ba abin mantawa cikin sauri ba ne.

Donald Tusk ya bukaci Amurka ta tuna irin zaratan dakarun sojin EU da suka rasa rayukansu a yakokin da ta yi da kasashe musamman a shekarar 2001 a Afghanistan.
Donald Tusk ya bukaci Amurka ta tuna irin zaratan dakarun sojin EU da suka rasa rayukansu a yakokin da ta yi da kasashe musamman a shekarar 2001 a Afghanistan. JOHN THYS / AFP
Talla

Shugaban kungiyar Tarayyar ta Turai Donald Tuska wanda ke amfani da damar taron na sabuwar yarjejeniya tsakanin EU da kuma Kungiyar tsaro ta NATO wajen sasanta rikicin da ke tsakanin kasashe mambobin kungiyar da Donald Trump, ya ce EU ta sadaukar da zaratan dakaru wajen taimakon tsaron Amurka.

Da ya ke jawabi ga Trump, Donald Tusk ya ce Amurka ba ta da abokiyar huldar da ta wuce EU don kuwa sadaukarwar da suka yi mata dama taimakon da su ke bata ya wuce gaban wadda Rasha ko kuma China ke mata.

Tuni shugaban Amurkan Donald Trump ya mayar da martini ga kalaman na Donald Tuska a sakon Twitter da ya wallafa, inda ya ce Amurka na kashe makudan kudade wajen baiwa EU kariyar tsaro musamman a kungiyar NATO, amma kuma batun haraji na neman zama matsala duk kuwa da cewa Amurkan na asarar akalla dala biliyan 151 a kasuwancin da ke tsakaninta da EU.

A sakonsa na biyu da ya wallafa Donald Trump ya ce dole ne Amurka ta biya haraji kankani su kuma kasashen na EU su biya da yawa la’akari da hidimar da ta ke musu.

Sai dai Donald Tusk ya ce, Amurka ta tuna irin rayukan sojojin EU da suka salwanta a shekarar 2001 .

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.