rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Zaben Amurka Donald Trump Birtaniya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Babu wanda zai iya kada ni a zaben 2020 - Trump

media
Shugaban Amurka Donald Trump, tare da Sarauniyar Ingila Elisabeth, bayanda ya kai ziyara kasar Birtaniiya. REUTERS/Kevin Lamarque

Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana aniyar sake neman wa’adin shugabancin kasar na biyu a zaben 2020.


Jaridar Mail da ake wallafawa a Birtaniya ta rawaito shugaba Trump da ke ziyara a kasar na cewa zai nemi tazarcen ne, la’akari da cewa kowa na son ganin ya ci gaba da shugabanci, kuma babu wani dan takara musamman daga jami’iyyar adawa ta Democrats, da zai iya kayar da shi a zaben shugabancin na Amurka mai zuwa.

Kafin tashi daga Birtaniyar dai zuwa kasar Finland don ganawa da shugaban Rasha Vladmir Putin, Trump ya karya ka’idar Birtaniya na sirranta ganawar da shugabanni suka yi da sarauniya Elizabeth, inda ya bayyanawa duniya batutuwan da suka tattauna akai da ita, musamman kan kalubalen da kasar ke fuskanta kan shirinta na ficewa daga karkashin kungiyar tarayyar turai.