Isa ga babban shafi
Spain

Jami'an Spain sun ceto sama da 'yan ci rani 340 daga teku

Jami’an gabar ruwan Spain sun yi nasarar ceto sama da ‘yan ci rani 340 daga hallaka a tekun Mediterranean a jiya Asabar, ciki harda wani mutum guda daga arewacin Afrika, da yake kokarin tsallaka tekun haye kan wata tayar babbar mota da aka dora kan katako mai matsakaicin fadi.

Wasu bakin-haure da ke kokarin tsallaka tekun Mediterranean zuwa turai.
Wasu bakin-haure da ke kokarin tsallaka tekun Mediterranean zuwa turai. Reuters
Talla

A halin yanzu alamu na nuni da cewa bakin-hauren da ke kokarin tsallakawa turai, sun sauya alkibilarsu zuwa kasar Spain a maimakon Italiya a baya.

Kusan makwanni biyu da suka gabata kungiyar EU, ta bayyana fargabar cewa Spain ka iya zama sabon mashigin da bakin-haure za su rika kwarara zuwa nahiyar, la’akari da yawan wadanda suka isa kasar a wannan shekara.

Alkalumman baya bayan nan da hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta duniya IOM ta wallafa, sun nuna cewa akalla bakin-haure dubu 16, da 902 ne suka isa kasar Spain a wannan shekara kadai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.