Bakonmu a Yau
Umar Elh Hachim kan isowar tawagar 'yan kwallon Faransa gida
Wallafawa ranar:
Kunna - 03:36
Dazun nan ne kungiyar kwallon kafar Faransa ta samu isowa kasar baya ga lashe kofin kwallon kafa na Duniya a Rasha a karawar da ta yi Croatia da ci 4 da 2.Jirgin da ke dauke da yan wasan ya sauka a filin tashi da saukar jirage na Roissy inda duban mutane daga sassa daban daban na kasar suka bukaci ganewa idanu bukukuwan da aka shirya a kai. Shugaban kasar da jami’an gwamnatin Faransa sun shirya tsaf domin tarben yan wasan a fadar Elysse kamar dai yadda za ku ji a tatauunawar mu da Umar Elh Hachim da ke dab da fadar Shugaban kasar Faransa.