rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Japan Tarayyar Turai

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Sabuwar yarjejeniyar kasuwanci tsakanin Japan da Turai

media
Yarjejeniyar kasuwanci tsakanin Japan da kungiyar kasashen Turai a Tokyo Reuters

Kasar Japan ta sanya hannu kan wani gagarumin shirin kasuwancin bai daya da kungiyar kasashen Turai wanda ke nuna yatsa ga kasar Amurka kan matakan da take dauka na yiwa yarjejeniyar kasuwancin tsakanin kasashen Duniya tarnaki.


Sabuwar yarjejeniyar dake zuwa tsakanin Japan da kasashen Turai na zuwa ne bayan da Shugaban Amurka Donald Trump ke bayyana cewa Amurka ba za ta amince da abinda ya kira 'makafin' yarjeniyoyin kasuwanci ba.

Ita dai wannan yarjejeniya a kulla ta ne a birnin Tokyo wanda zai kauda duk wani kudin fito kan motocin Japan da kuma chukwin da Faransa ke samarwa.

Shugaban kungiyar kasashen Turai, Donald Tusk ya bayyana yarjejeniyar a matsayin gagarumin sako ga shugaban Amurka Donald Trump.