Isa ga babban shafi
Faransa

Fadar Elyseé za ta kori babban dogarin Macron daga bakin aiki

Fadar shugaban kasa a Faransa, ta ce ta na shirye-shiryen korar babban dogarin shugaba Emmanuel Macron, bayan fitowar wasu faifan bidiyo da ke nuna jami'in na jibgar wani matashi a cikin masu zanga-zangar da ta gudana ranar 1 ga watan Mayun da ya gabata. Fadar ta bayyana batun da mafi munin cin mutuncin bil'adama karkashin shugabancin Emmanuel Macron. 

Faifan bidiyon na biyu ya nuna yadda babban dogarin shugaban ke kokawa da wata mace inda har ya kai ta kasa.
Faifan bidiyon na biyu ya nuna yadda babban dogarin shugaban ke kokawa da wata mace inda har ya kai ta kasa. Lionel BONAVENTURE / AFP
Talla

A wani bidiyon da wasu jaridun Faransa suka wallafa cikin wannan makon ya nuna yadda babban dogarin na Macron Alexandre Benalla sanye da hular kwano ta jami'an 'yan sanda na lakadawa wani matashi dukan kawo wuka tare da tattakashi da takalmi yayin zanga-zangar.

Yanzu haka dai Benalla na tsare domin amsa tambayoyi, inda masu gabatar da kara a birnin Paris ke bukatar ya amsa tuhuma kan amfani da hular kwanon 'yan sanda duk da kasancewarsa ba dan dan sanda ba.

Wata majiya ta kusa da ofishin masu binciken ta ce, hukumomi a Faransar sun kuma dakatar da wasu jami'an 'yan sanda uku, wadanda suma za su amsa tambayoyi kan zargin su da taimakawa Benalla da faya-fayan bidiyon zanga-zangar ta ranar 1 ga watan Mayu, don ya samu hujjojin da zai kare kan sa da su.

Ofishin shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron da ke fadar Elyseé, ya ce matakin korar Alexandre Benalla ya biyo bayan sake kallon wani faifan bidiyon wanda Ofishin ya bayyana da mafi munin cin zarafin bil'adama a mulkin na Emmanuel Macron.

Faifan bidiyon na biyu ya nuna yadda babban dogarin shugaban ke kokawa da wata mace inda har ya kai ta kasa.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.