rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Girka

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Gobarar daji ta hallaka akalla mutane 50 a Girka

media
Yanzu haka dai jami’an agaji na ci gaba da kai dauki don ceto mutanen da garuruwansu ke gab da dazuka. REUTERS

Adadin mutanen da suka mutu a gobarar dajin Girka ya tasamma 50 yau Talata, bayan da kungiyar bayar da agajin gaggawa ta RedCross ta kara gano gawar akalla mutane 26.


Kafin yanzu dai hukumomi a kasar ta Girka sun sanar da mutuwar akalla mutane 24 tare da wasu 150 kuma da suka jikkata, sai dai bayan gano sauran gawakin mutanen 26 a kauyen Mati addain ya karu zuwa 50.

Mai Magana da yawun gwamnatin Girka Dimitris Tzanakopoulos ya ce wutar wadda ta faro daga dazuka ta warwatsu ne zuwa wasu sassa na garuruwan da ke gab da dajin dama wuraren shakatawa da ke bakin teku.

A cewarsa galibin wadanda gobarar ta lahanta an same su ne ko dai a cikin gidajensu ko kuma a motoci yayin da wasu kuma gobara ta sanyasu fadawa teku.

Yanzu haka dai jami’an agaji na ci gaba da kai dauki don ceto mutanen da garuruwansu ke gab da dazuka.

Haka zalika jami’ai da dama sun bazu don kai daukin kashe gobarar musamman ga yankunan da ke makwabtaka da manyan dazukan da ke fuskantar gobarar.