Isa ga babban shafi
Turai-Gobarar Daji

Ruwan sama ya sanyaya tsananin zafin da ake fuskanta a Turai

Saukar ruwan sama kamar da bakin kwarya a wasu yankuna na Nahiyar Turai ya saukaka tsananin zafin da ake fuskanta sakamakon gobarar dajin girka da ta hallaka mutane 82 tare da jikkata da dama.

Yanzu haka dai akwai dazuka da dama a kasashen da ke ci gaba da cin wuta ba tare da jami'an kashe gobara sun iya yin nasarar kashe su ba.
Yanzu haka dai akwai dazuka da dama a kasashen da ke ci gaba da cin wuta ba tare da jami'an kashe gobara sun iya yin nasarar kashe su ba. Reuters/路透社
Talla

Tsananin zafin da tsakar ranar yau juma'a ya tilastawa jami'an kashe gobara dakatar da ayyukansu yayin da hukumomi a wasu sassa na nahiyar Turai suka haramta bude duk wasu guraren gashi a dai dai mlokacin da al'umma ke ci gaba da galabaita saboda zafin.

Sai dai bayan sakkowar ruwan sama a kasashe irinsu Girka, Faransa da  Jamus, Birtaniya, Sweden da Holland da kuma Latvia baya ga Belgium da Finland dama Switzerland an samu raguwar zafin wanda ke da alaka da mummunar gobarar dajin da ake fuskanta a Girka.

A birtaniya rahotanni sun ce an dakatar da sufurin wasu jiragen kasa saboda tsananin zafin bayan gargadin da masana yanayi suka yi bayan da karfin zafin ya kai maki 38.5 a ma'aunin zafi.

Haka zalika Sweden wadda har yanzu akwai sauran dazuka 17 da ke ci gaba da cin wuta ta haramta bude guraren gashi dama tafiye-tafiye masu nisa.

A Holland kuwa an yi ittifakin tsananin zafin ya ninka na 2017 wanda ya faru sanadiyyar gobarar daji har sau dubu 1 da 143.

Kasashen na Nahiyar Turai na fama da barazanar gobarar daji wadda a lokuta da dama jami'ai kan gaza shawo kan su, inda yanzu haka akwai dazuka da dama wadanda ke ci gaba da cin wuta ba tare da an iya kashe su ba.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.