Isa ga babban shafi
Amurka

Gobarar daji ta kone fadin kasa sama da kadada dubu 80

Gwamnatin Amurka ta aike da kayayyakin agaji zuwa jihar California, Jami’an kashe gobara ke kokain shawo kan mahaukaciyar wutar dajin da zuwa yanzu tayi sanadin hallakar mutane 6, tare da kone daruruwan gine-gine.

Wani yanki na jihar California da ke Amurka, da gobarar daji ta kone. 27 ga watan Yuli, 2018.
Wani yanki na jihar California da ke Amurka, da gobarar daji ta kone. 27 ga watan Yuli, 2018. REUTERS/Fred Greaves
Talla

Akalla mutane dubu 7000, gobarar ta tilastawa tserewa daga muhallansu a jihar da taimakon jami’an agaji, bayan da gobarar dajin ta kara fadada kusan ninki biyu, bisa yankin da ta mamaye a baya.

Gobarar dajin wadda ta tashi tun a ranar 23 ga watan Yuli da muke ciki, zuwa yanzu ta mamaye fadin kasa da ya zarta kadada dubu 80,906.

Sama da ‘yan kwana kwana dubu 1, 300 ne ke ci gaba da fafutukar kashe gobarar, wadda ke bazuwa cikin sauri.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.