rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Amurka Muhalli Canjin Yanayi

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Gobarar dajin California na barazana ga yankuna masu yawan jama'a

media
Gobarar daji yayin da ta mamaye tsaunukan Santiago, da ke jihar California, 6 ga watan Agusta, 2018. REUTERS

Jami’an kwankwana da ke fafutukar kashe gobarar dajin da ta lashe fadin kasa mai yawa a jihar California, sun bada umarnin kwashe dubban mutane daga gidajensu, a dai dai lokacin da gagarumar gobarar ke dada matsar inda jama’a ke da yawa.


Jami’an sun ce kwashe jama’ar ya zama tilas, la’akari da yadda iskar yankin ke dada gurbacewa a dalilin hayakin da gobarar dajin ke fitarwa, musamman a yankin arewacin jihar ta California.

Zuwa yanzu dai jami’an kwankwana sun sanar da samun nasarar shawo kan kashi 51 na gobarar dajin a arewacin jihar, bayan da ta kone kadada akalla dubu 180,000 na fadin kasa, tare da sanadin hallakar jami’an kwana kwana uku da fararen hura biyar.

Sama da jami’an kwana-kwana dubu 14,000 ne har yanzu ke fafutukar kawo karshen gobarar, wadda ta tilastawa mutane sama da dubu 21,000 tserewa daga gidajensu.