Isa ga babban shafi

An jikkata mutane 450 a zanga-zangar Romania

‘Yan kasar Romania akalla 50,000, sun ci gaba da gudanar da zanga-zangar neman kawo karshen gwamnatin kasar, bisa dalilansu na cewa matsalar cin hanci da rashawa ta yiwa masu rike da mukaman siyasa katutu.

Masu zanga-zanga a Romania yayin arrangama da jami'an tsaro.
Masu zanga-zanga a Romania yayin arrangama da jami'an tsaro. (Foto: Reuters)
Talla

Zanga-zangar wadda ta soma karfafa daga ranar Juma’ar da ta gabata, ta biyo bayan yunkurin da wasu 'yan siyasar kasar suka soma, na soke wasu tarin laifuka cin hanci da rashawa tare da hallata su.

A ranar Asabar, 11 ga watan Agusta 2018, akalla masu zanga-zanga sama da dubu 40 ne suka yi dandazo a gaban ofisoshin gwamnatin a Bucharest, babban birnin kasar ta Romania inda suke neman murabus din daukacin masu rike da mukaman siyasa.

Zuwa yanzu dai an jikkata mutane 450 daga cikin masu zanga-zangar, yayinda aka yiwa ‘yan sanda 30 rotse, sakamakon kazamar arrangamar da aka yi tsakanin bangarorin biyu.

Tun a farkon shekarar 2017 da jam’iyyar Social Democrats da karbi gwamnatin kasar, dubban ‘yan Romania ke gudanar da zanga-zangar lumana, sakamakon yunkurin da jam’iyyar ta ke yi na hallata wasu laifukan da suka shafi cin hanci da rashawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.