Isa ga babban shafi
Italiya

Babbar gada ta rufta da motoci a Italiya

Wata babbar gadar motoci ta rufta a kusa da birnin Genoa da ke Italiya, abin da ya yi sanadiyar faduwar kanana da manyan motoci daga saman gadar.

Gadar Morandi da ta rufta da motoci a birnin Genoa na Italiya
Gadar Morandi da ta rufta da motoci a birnin Genoa na Italiya Handout / ITALIAN POLICE / AFP
Talla

Ministan Sufuri na kasar, Danilo Toninelli ya bayyana fargabar samun gagarumin ibtila’i sakamakon ruftawar gadar, yayin da jami’an ‘yan sanda ke cewa, kawo yanzu akalla mutane 10 sun rasa rayukansu.

Jami’an ‘yan sandan sun alakanta aukuwar lamarin da barkewar iskar hadari mai karfin gaske.

Jami’an agaji da suka hada da na kashe gobara na ci gaba da aikin ceto kuma tuni suka garzaya da wadanda suka samu rauni asibiti

Tun a tsakankanin shekarar 1960 aka gina gadar da aka fi sani da gadar Morandi, yayin da tsawon mita 200 na gadar ya rufta a ranar Talata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.