Isa ga babban shafi
Italiya

Kasashen Turai sun jajantawa Italiya kan rushewar gada

Babbar gadar motoci da ta rufta a kusa da birnin Genoa da ke Italiya ta yi sanadiyar mutuwar akalla mutane sama da 30, abin da ya yi sanadiyar faduwar kanana da manyan motoci daga saman gadar.

Gadar Morandi da ta rufta da motoci a birnin Genoa na Italiya
Gadar Morandi da ta rufta da motoci a birnin Genoa na Italiya ANDREA LEONI / AFP
Talla

Ministan Sufuri na kasar Italiya, Danilo Toninelli ya bayyana fargabar samun gagarumin ibtila’i sakamakon ruftawar gadar, yayin da jami’an ‘yan sanda ke cewa, kawo yanzu akalla mutane 30 sun rasa rayukansu.

Jami’an ‘yan sandan sun alakanta aukuwar lamarin da barkewar iskar hadari mai karfin gaske.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya aike da sako zuwa hukumomin Italiya cewa,Faransa zata aikewa da ma'aikantan agaji zuwa kasar Italiya.

Shugaban gwamnatin Italiya Giuseppe Conte ya bayyana cewa zai ziyarci wurin da hatsarin ya auku a Genes dake arewacin kasar.

Jami’an agaji da suka hada da na kashe gobara na ci gaba da aikin ceto kuma tuni suka garzaya da wadanda suka samu rauni asibiti

A shekarar ta 1960 aka gina gadar da aka fi sani da gadar Morandi, yayin da tsawon mita 200 na gadar ya rufta a ranar Talata.

Kasashen turai da dama ne suka aike da sakon jaje da nuna alhinin su a yau talata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.