Isa ga babban shafi
SWEDEN

Manyan jam'iyyun Sweden sun yi kan-kan-kan

Bisa dukkan alamu, kasar Sweden ta kama hanyar kafa Majalisar Dokokin da manyan jam’iyyun siyasar kasar biyu ke da rinjaye iri daya bayan jam’iyyar Social Democrats ta samu karin goyon baya a zaben da aka gudanar a karshen mako. Kasar wadda aka san ta da sassaucin ra’ayi a Turai, yanzu haka ta zama mai tsattsauran ra’ayi saboda kwararar bakin haure.

Wasu daga cikin masu kada kuri'a a zaben Sweden
Wasu daga cikin masu kada kuri'a a zaben Sweden REUTERS/Ints Kalnins
Talla

Jam’iyyun masu tsattsauran ra’ayi na samun gagarumin rinjaye a 'yan shekarun nan a nahiyar Turai sakamakon fargabar kwararar bakin haure musamman daga yankin Gabas ta tsakiya da kuma arewacin Afrika.

A shekarar 2015, Sweden mai yawan al’umma miliyan 10 ta karbi baki kimanin dubu 163, matakin da ake ganin ya raba kan masu kada kuri’u tare wargaza tsarin cimma yarjejeniyar siyasa tsakanin jam’iyyu.

Yanzu haka an kidaya kuri’un kusan daukacin mazabun kasar, in da hadakar jam’iyyar Social Democrats mai mulki ke da kashi 40.6 cikin 100, yayin da jam’iyyar adawa ta Alliance ke da kashi 40.3

Wannan sakamakon ya nuna cewa, Social Democrat ta samu kujeru 144 daga cikin kujeru 349, yayin da Alliance ta samu kujeru 142, abin da ke nuna cewa za a shafe tsawon makwanni kafin samun kafaffiyar gwamnati.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.