Isa ga babban shafi
Rasha-Birtaniya

'Yan Rasha 2 da Birtaniya ke zargi da harin guba sun kare kansu

Mutane biyu 'yan kasar Rasha da Birtaniya ke zargi da kai harin guba kan Sergei Skripal sun wanke kansu a wata tattaunawa ta gidan talabijin mallakin Rashan inda suka ce yawon bude ido ya kai su birnin Salisbury ba kai hari ba. Sai dai fadar gwamnatin Birtaniyan ta Downing Street ta yi watsi da batun wanda gidan Talabijin mallakin Rasha na RT ya yi da mutanen 2 da aka bayyana a matsayin wadanda ake zargi da kai harin kan tsohon jami’in leken asirin Moscow da ya koma aiki da Birtaniya.

Alexander Petrov da Ruslan Boshirov su ne mutane biyu da Birtaniyan ta wallafa hotonsu tare da zargin cewa su ne suka isar da sakon na Rasha wajen kaddamar da harin gubar kan Skripal.
Alexander Petrov da Ruslan Boshirov su ne mutane biyu da Birtaniyan ta wallafa hotonsu tare da zargin cewa su ne suka isar da sakon na Rasha wajen kaddamar da harin gubar kan Skripal. 路透社。
Talla

Mai magana da yawun Firaminista Theresa May, ta ce tattaunawar wadda aka gina akan karya da birkita tunanin al’umma tsantsar yaudara ce da ke da nufin yawo da hankali mutane don kare kasar ta Rasha wanda kuma tuni Birtaniya ta yi watsi da shi.

Tashar Talabijin din ta RT news ta zanta da mutanen biyu wadanda aka bayyana sunanyensu da Alexander Petrov da kuma Ruslan Boshirov ta ce su ne Birtaniyar ta wallafa hotonsu tare da zargin cewa su suka isar da sakon Rashan wajen kai harin da guba kan tsohon jami’in leken asirin wanda ya koma aiki da Birtaniyar da ke zaune a birnin Salisbury.

Yayin zantawar wadda Talabijin din ta shafe mintuna 25 tana yi da mutanen biyu sun bayyana cewa sun shiga garin Salisbury ne kawai don yawon bude ido amma ba su da wata masaniya game da harin kan Sergei Skripal da ‘yarsa Yulia.

Tattaunawar wadda aka nade ta shekaran jiya Laraba tare da yada ta a jiya Alhamis ta zo ne sa’o’I kalilan bayan Shugaba Vladimir Putin ya sanar da gano mutanen biyu da Birtaniya ta nuna hotunansu a matsayin wadanda suka kai harin, inda ya bukace su da shaidawa manema labarai ainahin abin da ya kai su birnin na Salisbury.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.