rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Faransa Zaben Faransa Emmanuel Macron

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Ministan Cikin Gidan Faransa na dab da murabus

media
Shugaban Faransa Emmanuel Macron da Ministan Cikin Gidan Kasar Gérard Collomb Alberto PIZZOLI / AFP

Ministan Harkokin Cikin Gidan Faransa, Gerard Collomb ya sanar da shirinsa na ajiye mukaminsa bayan zaben Majalisar Dokokin Tarayyar Turai a shekara mai zuwa, matakin da zai dada haifar da cikas ga gwamnatin shugaba Emmanuel Macron.


Collomb da ke cikin manyan ministocin Macron na gaban-goshi ya shaida wa mujallar L’Express cewa, zai yi murabus don samun damar takarar neman kujerar magajin garin birnin Lyon da ke kudancin Faransa a shekarar 2020.

Collomb ya ce, duk da dai akwai sauran lokacin gudanar da zaben kananan hukumomi, amma akwai bukatar samun isasshen lokacin gudanar da yakin neman zabe.

Collomb mai shekaru 71 ya taba rike mukamin magajin garin birnin Lyon, in da ya shafe tsawon shekaru 16 kan karaga har sai da Macron ya nada shi Minista.

Wannan na zuwa ne makwanni uku da murabus din Ministan Muhallin kasar mai farin jini, Nicolas Hulot, lamarin da ya sosa ran gwamnatin shugaba Macron wanda karbuwarsa a idon Faransawa ta ragu.