Isa ga babban shafi
Turai

Batun bakin haure ya mamaye taron shugabannin Turai a Salzburg

Shugabannin yankin Turai za su shiga tattaunawa da kasar Masar da sauran kasashen Arewacin Afirka domin tunkarar matsalar kwararar baki da ke shiga Turai ba a kan ka’ida ba.

Shugaban gwamnatin Austriya Sebastian Kurz da Firaministar Birtaniya Theresa May a taron Salzbourg, 19 satumba 2018.
Shugaban gwamnatin Austriya Sebastian Kurz da Firaministar Birtaniya Theresa May a taron Salzbourg, 19 satumba 2018. REUTERS/Leonhard Foeger
Talla

Sebastian Kurz Firaministan Austria da ke daukar nauyin taron shugabannin yankin a birnin Salzburg, ya ce tuni Masar ta tabbatar masu da cewa za ta saurari bukatunsu.

A shekara ta 2015 sakamakon yadda aka samu kwararar dimbin baki zuwa yankin Turai, kungiyar ta EU ta kulla yarjeniyoyi da kasashen Turkiyya da Libya kan wannan batu, to sai dai ga alama matafiyan na ci gaba da sauya dubaru domin shiga yankin na Turai, ciki har da canza hanyoyin da suka saba amfani da su.

A yau Alhamis an shiga rana ta biyu a taron da shugabannin kasashen na EU ke gudanarwa a birnin na Salzburg inda suke tattaunawa kan matsalar ‘yan ci rani da kuma batun janyewar Birtaniya daga cikin kungiyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.