Isa ga babban shafi
Jamus

Kawancen Merkel ya sha kaye a zaben Jamus

Jam’iyyar SCU da ke kawance da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta sha mummunar kaye a zaben 'yan majalisun da aka gudanar a yankin Bavaria, abin da ake ganin zai raunana kawancen jam’iyyu 3 da suka kafa gwamnatin kasar.

Shugabar Gwamnatin Jamus, Angela Merkel
Shugabar Gwamnatin Jamus, Angela Merkel Fuente: Reuters.
Talla

Jam’iyyar Christian Social Union ta samu kashi 37 ne na kuri’un da aka kada, wanda ya nuna cewar ta rasa kashi 10 daga sakamakon da ta samu shekaru 4 da suka gabata a Jihar da take jagoranci ita kadai tun daga shekarar 1960.

Sakamakon zaben ya nuna cewar, yanzu haka sai jam’iyyar ta shiga kawance da wata kila jam’iyyar masu sassaukar ra’ayi wadda ta samu kashi 11 kafin kafa gwamnati a Yankin.

Jam’iyya ta 3 da ke kawance da Merkel ta Social Democrats ta samu sama da kashi 9 da rabi, abin da ya nuna cewar Jam’iyyar Green Party ce ta biyu mafi girma a yankin.

Shugaban CSU Markus Soeder ya bayyana takaicinsa da sakamakon, yayin da Ministan Cikin Gida, Horst Seehoofer ya bayyana ranar Litinin a matsayin ranar bakin ciki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.