Ambaliyar ruwa ta kashe mutane a Faransa
Akalla mutane 13 sun rasa rayukansu sakamakon amabaliyar ruwa da ta afka wayankin Kudu maso Yammacin Faransa.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Gwamnatin Yankin Aude ta ce, an samu asarar rayuka hudu ne a garin Villegailhenc, in da ambaliyar dauke da laka ta yi kamari.
Firaministan Kasar, Edouard Philippe ya bayar da jumullar alkaluman mutane 13 da suka rasa rayukansu a ibtila’in wanda ya auku a cikin daren daya gabata.
Koda yake ana fargabar cewa, ambaliyar ta yi awon gaba da wasu gawarwakin kamar yadda al’ummar yankin ke cewa.
An kuma samu tinbatsar kogi a garin Conques-sur-Orbiel, in da zurfin ruwan kogin ya karu da fiye da mita 6.
Tuni mahukuntan kasar suka bukaci jama’a da su zaune a cikin gidajensu, yayin da aka rufe makarantu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu