rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Faransa Korea ta Kudu

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Shugaba Macron ya gana da Shugaban Koriya ta kudu

media
Shugaban Faransa Emmanuel Macron tareda Shugaban Koriya ta Kudu Moon Jae In a Faransa PHILIPPE WOJAZER / POOL / AFP

Shugaban Koriya ta Kudu Moon Jae-in ya gana da Shugaban Faransa a fadar Elysee dake birnin Paris, inda Shugabanin biyu suka tattauna dangane da batutuwa da suka shafi Diflomasiya, Cinikaya da kuma rage dumamar yanayi a Duniya.


Shugaba Macron ya bayya farin cikinsa kan ziyarar ta Shugaban Koriya ta kudu da kuma jajantawa Faransawa dangane da ambaliyar da ta afka musu.

A cewar Macron Faransa da Korea ta Kudu na bukatar sake duba hanyoyin fasalta tsarin cinikaya da hulda ta kusa da kasashen duniya kamar yadda dokkokin suka tanada.

Zalika Macron y ace za su mayar da hankali wajen sake duba batutuwan da suka shafi sadarwa, da kuma batun yaki da dumamar yanayi a Duniya.

Ziyarar ta Moon Jea-in na zuwa ne bayan ganawa ta musaman da yayi da manyan jami`an gwamnatin Jamus a Hambourg.