rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Birtaniya Tarayyar Turai

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

An gaza cimma matsaya tsakanin Birtaniya da EU a Brussels

media
Gaza cimma matsaya a taron na Brussels na nuni da cewa har yanzu tsugune bata karewa Birtaniya ba. REUTERS/Peter Nicholls

Shugabannin kungiyar Kasashen Turai sun jingine sake wani taro a watan gobe domin kammala batun ficewar Birtaniya daga kungiyar saboda gaza cimma matsaya a shirye-shiryen ficewar bayan taron da ya gudana a Brussels tare da Firaministar Birtaniyan.


Theresa May wadda ta yi kusan mintuna 15 ta na yi wa majalisar bayanin inda aka kwana game da ficewar, Shugaban Majalisar Kungiyar Turai Antonio Tajani wanda ya ke dakin ya bayyana cewa babu komi cikin jawabin.

Sai dai kuma shugabannin kasashen kungiyar sun nemi a ci gaba da tattaunawa, ba tare da kwakkwarar bayani ba ko yaya ake ciki game da taron watan gobe da ake ganin zai kasance mai muhimmanci game da makomar ta Birtaniya.

Wannan ya kasance matakin da zai gamsar da Theresa May wadda ke fuskantar matsin lamba a kasarta daga masu bukatar ficewar kasar daga Tarayyar Turai, da kuma masu hangen cewa kasada ce ficewar ta su.

Gaza cimma matsaya a taron na Brussels na nuni da cewa har yanzu tsugune bata karewa Birtaniya ba, haka zalika babu wani cikakken kwarin gwiwa game da ficewar ta ta a karshen watan 3 na sabuwar shekara.

Akwai dai fargabar cewa muddin babu tanadi sosai bayan ficewar Birtaniyar daga EU to shakka babu za’a iya fuskantar tarin matsaloli da za su biyo baya.