rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Faransa Tarayyar Afrika

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Sarkozy shugaba na 3 da ake tuhuma da laifukan cin hanci da rashawa

media
Nicolas Sarkozy tsohon Shugaban kasar Faransa RFI

Kotun daukaka kara a Faransa, ta ce dole sai tsohon shugaban kasar Nicolas Sarkozy ya kare kansa dangane da zargin karbar kudaden yakin neman zabe ta hanyoyin da suka saba wa dokokin kasar a shekara ta 2012.


Sarkozy mai shekaru 63 a duniya, ya ce zai sake daukaka kara dangane da wannan batu, kamar dai yadda dokokin kasar suka ba shi damar karshe domin yin haka.

Masu shigar da kara na zargin tsohon shugaban ne da kashe kudaden da yawansu ya kai Euro milyan 43 a yakin neman zabensa, abin da ya yi hannun riga dokokin kasar da suka bayar da damar kashe abin da bai wuce Euro milyan 22 da rabi ba.

Baya ga zargin na kashe kudaden da suka wuce kima a 2012 akwai kuma tuhumar karbar wasu makudan kudade daga hannun tsohon shugaban Libya Mu’ammar Gaddafi don gudanar da yakin neman zabensa karon farko a 2007.