Isa ga babban shafi
Amurka

Dan bindiga ya hallaka mutane 11 a Amurka

Wani dan bindiga a Amurka na fuskantar tuhume-tuhume 29 da suka shafi aikata muggan laifuka, sakamakon bude wuta da yayi akan wani wurin Ibadar Yahudawa dake garin Pittsburg, inda ya hallaka mutane 11, da kuma jikkata wasu 6.

Jami'an tsaron Amurka, yayin sintiri a wurin bautar da dan bindiga ya hallaka mutane 11 a garin Pittsburgh. 27/10/18.
Jami'an tsaron Amurka, yayin sintiri a wurin bautar da dan bindiga ya hallaka mutane 11 a garin Pittsburgh. 27/10/18. REUTERS/John Altdorfer
Talla

Rahotanni sun ce dan bindigar Robert Bowers mai kimanin shekaru 46, ya soma ne da karajin cewa “tilas dukkanin yahudawa su mutu” kafin bude wuta kan masu Ibadar.

Daga bisani ne jami’an tsaro suka ci karfin dan bindigar bayan musayar wutar da suka yi, inda suka kamashi, aka kuma garzaya da shi asibiti don maganin raunukan da ya samu.

Daga cikin tuhume-tuhumen da dan bindigar ke fuskanta, akwai guda 11 kan yin amfani da makami wajen aikata kisan gilla, sai kuma tuhume-tuhume 11 kan aikata laifin kawo cikas ga ‘yancin gudanar da ibada.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.