Isa ga babban shafi
Faransa

Tsibirin New Caledonia ya zabi ci gaba da zama a Faransa

Al’ummar tsibirin Caledonia sun zabi ci gaba da kasancewa a karkashin kasar Faransa, bayan kada kuri’a a zaben raba gardama a wanna Lahadi, 4 ga Nuwamba, 2018.

Wasu daga cikin mazauna Nouméa babban birnin tsibirin New Caledonia, yayin kada kuri'a a zaben raba gardama kan neman 'yanci ko ci gaba da zama a karkashin Faransa. 04/11/2018.
Wasu daga cikin mazauna Nouméa babban birnin tsibirin New Caledonia, yayin kada kuri'a a zaben raba gardama kan neman 'yanci ko ci gaba da zama a karkashin Faransa. 04/11/2018. RFI / Julien Chavanne
Talla

Zaben raba gardamar na yau tamkar zakaran gwajin dafi ne kan goyon bayan da Faransa ke fatan ci gaba da samu daga yankuna ko tsibirai da dama, wadanda suke karkashin ikonta duk da cewa suna nesa da ita.

Sakamakon zaben raba gardamar ya nuna cewa kashi 59% daga cikin wadanda suka kada kuri’ar ne suka yi watsi da bukatar neman ballewar yankin na New Caledonia daga Faransa domin zama kasa mai cin gashin kanta.

Kafin zaben na yau dai, masu sharhi sun sa ran cewa sakamakon zaben na yau ka iya tabbata, la’akari da cewa kuri’ar jin ra’ayin ta nuna cewa akalla kashi 63 zuwa 70 da al’ummar tsibirin sun fi son zama a karkashin Faransa, lamarin da baya rasa nasaba da euro biliyan 1 da miliyan 300, da gwamnatin ta Faransa ke baiwa tsibirin a duk shekara.

Tsibirin New Celdonia mai nisan kilomita akalla dubu 18 daga Faransa, daya ne daga cikin yankunan duniya masu arzikin ma’adanin Nickel, wanda ake amfani da shi wajen samar da kayayyakin lantarki, inda ake samun akalla kashi daya bisa hudu na ma’adanin na Nickel da ake amfani da shi a duniya.

Kimanin mutane dubu 175,000 ne aka kiyasta sun kada kuri’a a zaben na yau, koda yake kafin wannan lokaci, wata kuri’ar jin ra’ayi ta nuna cewa mafi akasarin al’ummar tsibirin sun fi son zama a karkashin Faransa.

Sai dai akwai fargabar cewa, zaben rabar gardamar ka iya tayarda da tsimin kabilar Kanak ‘yan asalin tsibirin na New Celdonia, wadanda a baya suka yi fafutukar kwatar ‘yancinsu, yunkurin da ya haifar da kazamin rikici a tsibirin, cikin shekarar 1980, inda sama da rayuka 70 suka salwanta.

Rikicin ne ya tilasta cimma yarjejeniyar sulhu tsakanin masu rahin ‘yantar da tsibirin na New Celdonia da Faransa a shekarar 1998, wadda ta bada damar ci gaba da zaman yankin a karkashin ikon Faransa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.