rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Italiya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Ambaliyar ruwa ta hallaka mutane 30 a Italiya

media
Tuni dai hukumomi a kasar suka fara gargadin jama'a da su kauracewa yankunan da ake kyautata zaton samun ambaliyar. Rinsy XIENG / TWITTER / AFP

Adadin mutanen da suka mutu a Ambaliyar ruwan Tsibirin Sicily na kasar Italiya ya tasamma mutane 30 sabanin 12 da tun farko jami’an agaji suka sanar da safiyar yau.


A cewar hukumar bayar da agajin gaggawa ta Italiyan, cikin mutane 12 da suka mutu karon farko sanadiyyar ambaliyar ruwan, 9 daga ciki ‘yan gida guda ne ciki har da yaro mai shekara guda.

Yanzu haka dai akwai yankuna 6 na kasar ta Italiya da ke fuskantar barazanar ambaliyar ruwan, yayinda hukumomi ke ci gaba da aikin ceto a yankunan da ambaliyar ta tsananta musamammn yankin Palermo wanda ke gab da teku.