Macron ya yaba da sakamakon zaben tsibirin Caledonia
Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya yaba da matakin yankin Caledonia na kada kuri’ar ci gaba da kasancewa karkashin Faransa a yau Lahadi.
Wallafawa ranar:
Cikin wasu jawabai da ya gabatar jim kadan bayan fitowar sakamakon zaben raba gardamar yankin na Caledonia, Macron ya ce abin alfahari ne ga Faransa a yau dama makomarta a gobe, kan yadda yankin ya zabi ya ci gaba da kasancewa matsayin kasa dunkulalliya tare da Faransa.
Sakamakon zaben yankin ya nuna cewa kashi 70 cikin dari na al’ummar yankin na fatan ci gaba da kasancewa karkashin Faransa, ko da dai ana ganin hakan baya rasa nasaba da euro biliyan 1 da miliyan 300, da gwamnatin ta Faransa ke baiwa tsibirin na New Caledonia duk shekara.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu