rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Afghanistan Rasha Taliban

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Taliban za ta halarci tattaunawar sulhu da Afghanistan a Moscow

media
Shugaban Afghanistan Ashraf Ghani a birnin Kabul. 15/07/2018. REUTERS/Mohammad Ismail

Rasha ta ce shugaban Afganistan Ashraf Ghani, ya amince zai aika da tawagar manyan jami’an diflomasiyyar kasar domin halartar tattaunawar sulhu da kungiyar Taliban a karkashin jagorancin kasar ta Rasha a birnin Moscow.


Wannan dai shi ne karo na farko da sashin diflomasiyyar mayakan Taliban zai halarci irin wannan tattaunawa ta sulhu.

Tun a watan Agustan da ya wuce, Rasha ta yi yunkurin ganin tattaunawar ta gudana, inda ta gayyaci kasashe 12 da kungiyar ta Taliban, amma shugaba Ashraf Ghani yayi watsi da tayin, inda ya ce tilas sai dai tattaunawar ta gudana a karkashin jagorancin Afghanistan.

Ma’aikatar harkokin wajen Rasha ta ce tattaunawar za ta gudana a ranar 9 ga watan Nuwamban da muke ciki.

Wasu daga cikin kasashen da za su tura wakilcinsu wajen tattaunawar sun hada da India, Iran Pakistan, China da kuma Amurka.