Isa ga babban shafi
Macron-Turai

Macron ye nemi Turai ta daina sayen makaman Amurka

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya bukaci kasashen Turai su kaucewa kashe kasafin kudin su wajen sayen makaman Amurka, sakamakon cacar bakin da ta kaure tsakaninsa da shugaba Donald Trump.

Macron ya ce bayan yakin duniya na biyu, suna bukatar Amurka domin ba su tsaro, amma yanzu lokaci ya canja inda suke bukatar samarwa kan su tsaro.
Macron ya ce bayan yakin duniya na biyu, suna bukatar Amurka domin ba su tsaro, amma yanzu lokaci ya canja inda suke bukatar samarwa kan su tsaro. Francois Mori/Pool via REUTERS
Talla

Matakin ya biyo bayan sukar da Trump ya yiwa Macron kan bukatar san a kafa rundunar sojin kasashen Turai da zata dinga kare Yankin maimakon dogaro da Amurka.

Trump ya bayyana kalaman Macron a matsayin cin fuska ga Amurka.

A hirar da yayi da tashar CNN, shugaba Macron ya ce bai ga dalilin da zai sa kasashen Turai su kara kasafin kudin tsaron su don sayen makaman Amurka, inda ya soki shirin kasar Belgium na sayen jiragen saman yaki daga Amurka makon jiya maimakon sayen na Turai.

Macron ya ce bayan yakin duniya na biyu, suna bukatar Amurka domin ba su tsaro, amma yanzu lokaci ya canja inda suke bukatar samarwa kan su tsaro.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.