Isa ga babban shafi
Faransa- Belgium

Shugaba Macron na ziyarar aiki a Belgium

Shugaba Emmanuel Macron ya bukaci a kara kyautata alaka tsakanin Farsansa da Belgium, a ranar farko ta ziyarar aiki irinta ta farko da wani shugaban Faransa ya kai a cikin rabin karni a kasar.

Shugaba Emmanuel Macron da matarsa  Brigitte tare da Firaministan Belgium, Charles Michel
Shugaba Emmanuel Macron da matarsa Brigitte tare da Firaministan Belgium, Charles Michel REUTERS/Reinhard Krause
Talla

Macron na gudanar da wannan ziyara a Belgium ne a dai dai lokacin da yake fuskantar zanga-zangar nuna kiyayya da wasu matakai da yake dauka cikin gida Faransa, in da aka shiga rana ta hudu da jama’a ke gudanar da tarzomar rashin amincewa da karin kudin man fetur da kuma dangoginsa.

A ranar farko, Macron wanda ke tare da Uwargidansa Brigitte ya ziyarci biranen Brussels da kuma Gand, in da ya gana da Sarki Philippe da Sarauniya Mathilde a wannan kasa da ke da iyaka mai tsawon kilomita 620 tsakaninta da Faransa.

A ranar Talata kuwa, Macron zai gana ne da Firaministan Belgium Charles Michel, wanda duk da cewa jam’iyyunsu na da ra’ayoyi mabambanta, to amma kusan ra’ayoyinsu sun zo dai dai a fagen kare manufofin Kungiyar Turai.

Daga lokacin da ya dare kan karagar mulki zuwa yau, shugaba Macron ya ziyarci kasashe 19 daga cikin 27 na yankin Turai, kuma babban sakon da yake dauke da shi a kullum shi ne, samar Kungiyar Tarayyar Turai mai karfi domin tunkarar manyan kalubalen da ake fama da su a wannan zamani.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.