Isa ga babban shafi
Italiya

EU na gab da sanya wa Italiya takunkumin kudi

Hukumar Tarayyar Turai ta yi watsi da kasafin kudin Italiya, abin da ake kallo a matsayin matakin farko na sanya wa kasar takunkumi.

Mataimakin shugaban Hukumar Tarayyar Turai, Valdis Dombrovskis ya ce, Italiya za ta fada cikin mummunan hali
Mataimakin shugaban Hukumar Tarayyar Turai, Valdis Dombrovskis ya ce, Italiya za ta fada cikin mummunan hali REUTERS/Francois Lenoir
Talla

Matakin da Hukumar Tarayyar Turai mai shalkawata a birnin Brussels ta dauka kan Italiya bai zo da mamaki ba domin kuwa an zaci faruwarsa, kuma hakan na zuwa ne ‘yan makwanni da hukumar ta mayar da daftarin kasafin Italiya na shekarar 2019, tare da ba ta umarnin yi masa gyaran fuska.

Sai dai gwamnatin Italiya ta yi kunnan kashi da wanna umarni, in da ta tsaya kan bakarta ta kashe makudden kudade kamar yadda ke kunshe a daftarin kasafin.

A ranar Laraba ne, Hukumar Turan ta ce, a hukumace ta fara zaman duba wannan dambarwa da aka iya kaiwa ga sanya takunkuman kudade kan Italiya.

Mataimakin Kwaminshinan Hukumar, Valdis Dombrovskis ya ce, Italiya na fuskantar barazanar fadawa cikin wani mawuyacin hali.

A cewar Dombrovskis, har yanzu kofa a bude take don da tattaunawa kan yadda za a samu masalaha kan dambarwar, yayin da Firaministan Italiya, Giuseppe Conte ya ce, zai gana da shugaban Hukumar Turai, Jean Claude Juncker a ranar Asabar don gamsar da shi game da kasafin nasu.

Tarayyar Turan ta ki amince wa Italiya ne saboda tulin basukan da ke kan kasar, abin da mahukuntan kasashen da ke amfani da takardar kudin Euro ke cewa, zai shafe su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.