Arrangamar masu zanga-zanga da 'yan sanda ta kazanta a Paris
Shugaban Faransa Emmanuel Macron zai yiwa al’ummar kasar jawabi bayan kazamar arangamar da aka samu tsakanin masu zanga-zanga da jami’an tsaro.
Wallafawa ranar:
Macron ya bayyana damuwar sa kan irin tashin hankalin da ya gani lokacin arangamar.
Zuwa yanzu dai ‘yan sandan Faransa sun jefa gurnetin barkonon tsohuwa fiye da dubu 5 kan masu riguna dorowa da suka fito zanga-zanga shekaranjiya, yayinda kuma ‘yan kwana-kwana suka kashe fiye da wutar gobara 100, a tsakanin babban filin kasar da fadar shugaban kasa, inda masu zanga-zangar suka tafka barna sosai.
Yayin wata ganawa da mukarrabansa a ofishinsa, shugaba Macron ya bayyana damuwa matuka, lokacin da suka ga irin yadda jami’an tsaro da masu zanga-zangar suka shiga juna, tamkar a fage yaki.
Kakakin shugaba Macron, Benjamin Griveaux ya ce shugaban kasar, zai gabatar da jawabi a yau, kuma tuni ya yi korafi sosai a kan yan majalisar dokokin kasa da masu fada a ji da suka kasa fito da dubaru da hanyoyin hana faruwar rikicin.
Shugabanin jam’iyyun adawa da dama ne suka nuna gowon bayansu ga masu zanga-zangar, musamman babbar abokiyar hamayyar Macron, Marine Le Pen, wadda da ta jinjina musu ganin irin yadda cikin kwana 9 suka share kasar Faransa.
A jiya Litinin kotu ta saurari a shara’o’in mutane 10 daga cikin 101 da ‘yan sanda suka kama cikin zanga-zangar, wadda ta tara mutane akalla dubu 8 a birnin Paris kadai, inda kuma mutane 31 suka samu rauni, daga cikinsu jami’an ‘yan sanda 7.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu