Isa ga babban shafi
Faransa

Macron na nazarin maido da dokar ta baci a Faransa

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce gwamnatinsa ta soma nazari kan yiwuwar maido da dokar ta baci domin tabbatar tsaron rayuka da dukiyar al'umma, biyo bayan zanga-zangar da aka shafe makwanni uku dubban 'yan kasar na yi sanye da riguna kalar dorawa.

Masu zanga-zanga yayin arrangama da 'yan sanda a Paris.
Masu zanga-zanga yayin arrangama da 'yan sanda a Paris. REUTERS / Stéphane Mahe
Talla

Shugaba Macron ya bayyana haka ne jim kadan bayan soma taro da mukarraban gwamnatinsa a wannan Lahadi domin lalubo bakin zaren kawo karshen zanga-zangar adawa da karin farashin albarkatun mai da ta juye zuwa tarzoma.

Daruruwan masu zanga-zanga a ranar asabar sun cinnawa motoci masu yawa wuta, biyo bayan arrangamar da suka yi shafe tsawon ranar suna yi da jami’an tsaro a birnin Paris.

Jim kadan bayan soma zanga-zangar ce ta juye zuwa tarzoma, lamarin da yasa jami’an tsaro mayar da martani da hayaki mai sa hawaye, domin tarwatsa dandazon jama’ar dake kokarin yi musu rotse da duwatsu da sauran abubuwa masu hadari.

Zuwa yanzu dai jami'an tsaron Faransa sun kama mutane 500, bisa samunsu da laifin barnata dukiyar gwamnati da sauran jama'a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.