rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni Kwallon Kafa Ingila

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Ashley ya sha alwashin saida kungiyar Newcastle a karshen Disamba

media
Attajiri Mike Ashley da ya mallaki Newcastle United tare da matarsa, yayin kallon wasa tsakanin kungiyar da Tottenham na gasar Premier.13/12/15. Reuters/Toby Melville Livepic

Attajirin da ya mallaki kungiyar kwallon kafa ta Newcastle dake Ingila, Mike Ashley, ya ce a karshen watan Disambar da muke ciki zai saida kungiyar.


Ashley ya yanke shawarar saida Newcastle bayan shafe sama da shekaru 10 da sayenta.

A tsawon lokacin da ya attajirin ya shafe yana rike da kungiyar, Newcastle ta fuskanci durkushewa zuwa kasa da matakin gasar Premier ta Ingila sau biyu.

A shekarar 2007 Mike Ashley ya ya sayi kungiyar ta Newcastle kan kudi fam miliyan 134 da kusan rabi. A shekarar 2017 Ashley, yayi yukurin saida kungiyar ga wata attajira Amanda Staveley amma daga bisani ya fasa, bayan tayin biyan fam miliyan 300.

A halin yanzu Newcastle na kan matsayin ta 15 a teburin gasar Premier ta Ingila a karkashin horarwar Rafael Benitez.