Isa ga babban shafi
Jamus

Angela Merkel zata janye daga Shugabancin jam'iyyar CDU

Yau juma’a Angela Merkel za ta mika ramagar shugabancin jam’iyyar ta CDU a hannun wanda zai jagoranci jam’iyyar bayan share shekaru 18 tana rike da matsayin.Merkel mai shekaru 64 a duniya, za ta bar shugabancin jam’iyyar ne bayan da ta sha kashi sau da dama a zabubukan da suka gabata.

Angela Merkel Shugabar Gwamnatin Jamus
Angela Merkel Shugabar Gwamnatin Jamus REUTERS/Fabrizio Bensch
Talla

A watan Oktoba ne jam’iyyar SCU da ke kawance da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta sha mummunar kaye a zaben 'yan majalisun da aka gudanar a yankin Bavaria, abin da ake ganin zai raunana kawancen jam’iyyu 3 da suka kafa gwamnatin kasar.

Jam’iyyar Christian Social Union ta samu kashi 37 ne na kuri’un da aka kada, wanda ya nuna cewar ta rasa kashi 10 daga sakamakon da ta samu shekaru 4 da suka gabata a Jihar da take jagoranci ita kadai tun daga shekarar 1960.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.