rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Ecuador Tarayyar Turai

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Julian Asange ya cika sharuddan barin ofishin jakadancin Ecuado

media
Julian Assange,ce jagoran shafin Wikileaks REUTERS/Peter Nicholls/Foto de archivo

Shugaban kasar Ecuador ya ce jagoran shafin nan mai fallasa bayanan sirri da ake kira Wikileaks Julian Assange, ya cika dukanin sharuddan da aka gindaya masa kafin barin ofishin jakadancin kasar da ke birnin London.


Assange, mai shekaru 47 da haihuwa, ya sami mafakar siyasa a ofishin jakadancin kasar ta Ecuador da ke birnin London, tun a ranar 19 ga watan Yuni shekarar 2012, don kaucewa mika shi kasar Sweden, inda ake zargin shi da laifin yin fyade.

Assange yace ya na fargabar idan aka mika shi Sweden, daga can kuma za a iya mika shi Amurka, don a tuhume shi da laifin leken asiri.
Assange wanda dan asalin kasar Australia ne, ya share tsawon shekaru 6 boye a ofishin jakadancin kasar ta Ecuador .